21 Mayu 2021 - 13:35
​Araqchi: An Samu Gagarumin Ci Gaba A Tattaunawar Farfado Da Yarjejeniyar Nukiliya

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa, an samu gagarumin ci gaba a tattaunawar da aka gudanar tsawon makonni biyu a birnin Vienna.

ABNA24 : A zatawarsa da tashar talabijin ta NHK ta kasar Japan a yau a birnin Tehran, Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kuma shugaban tawagar Iran a tattaunawar farfado da yarjejeniyar nukiliyar da aka cimmawa kan shirin Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa, an samu gagarumin ci gaba a tattaunawar da aka gudanar tsawon makonni biyu a birnin Vienna na kasar Austria.

Araqchi ya ce tsawon makonni an gudanar da tattaunawa mai matukar wahala, amma dai za a iya cewa an cimma abubuwa da dama a wannan wannan zama, kuma Iran har yanzu tana kan bakanta na neman a janye mata dukkanin takunkuman da Amurka ta dora da suka shafi shirinta na nukiliya, wanda kuma a kan hakan tattaunawar take gudana.

Ya ci gaba da cewa, a halin yanzu dukkanin tawagogin kasashen ad suke halartar tattaunawa sun koma kasashensu domin shawara, kafin komawa zama na gaba a mako mai zuwa, inda ake sa ran amincewa da abubuwan da aka cimmawa tsakanin dukkanin bangarorin.

Sanann kuma Araqchi ya kara cewa, akwai wasu batutuwa da ba a riga an cimma daidaito a kansu ba, amma dai akwai fatan ganin an warware su, domin kuwa ita kanta Amurka ta fahimci muhimamncin kasancewarta cikin yarjejeniyar, kuma ga dukkanin alamu tana son dawowa.

342/